<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>90</hymn_number>
<title>Zamanin Da, Almasihu Ya Zo LW90</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zamanin da, Almasihu ya zo
 Duniya, cetonmu ne ya ke so.
 Kada mu kasa, mu dai, sai mu kai,
 Tare mu zauna da ainihin rai.

[V2]
 KORUS
 Wa'azin Yesu, shi mu ke yi,
 Shi mu ke yi, tsaya ka ji.
 Kada ka raina, kada ka ƙi,
 Riƙe da kyau, ka bi.

[V3]
 2) Iko ya karƃa a wurin Uba
 Domin ya taimake mu, shi ya sa
 Masu shan wuya da karkatattu
 Suka zo gunsa, ya hutad da su.
 Korus

[V4]
 3) Wa'adin Allah ya cika sarai,
 Nasa Ɗan Rago ya mutu sosai.
 Aibunsa babu, duk laifinmu ne,
 Ɗaukar zunubinmu mutuwa ce.
 Korus

[V5]
 4) Kwanansa uku a binne ya ke,
 Sai aka gan shi rayayye ne kuwa.
 Duba, ka ga Ubangiji ne shi,
 Sanadin ceto ne, shi za ka bi.
 Korus

[V6]
 5) Ina godiya ga Allah Mai Rai
 Domin ƙaunarsa a cikin Yesu.
 Ya ba da Ɗansa don zunubaina,
 Ya ba ni rai na har abada fa.
 Korus</lyrics>
</song>